in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya dage kan hadin kai tsakanin jam'iyyu a kasar Sin
2012-12-26 10:31:54 cri

Babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC, Xi Jinping ya ce, hukumomi za su ci gaba da tabbatar da tsarin hadin kai tsakanin jam'iyyu da kuma ba da cikakken goyon baya ga irin rawar da jam'iyyu wadanda ba na kwaminis ba ke takawa wajen sa ido kan harkar siyasa.

Babban sakatare Xi ya bayyana hakan ne a ranakun 24 da kuma 25 ga watan Disamba yayin wata ganawa da sabbin shugabannin jam'iyyun siyasa takwas wadanda ba na kwaminis ba, da kuma kungiyar tarayyar masu harkar masana'antu da cinikkaya na kasar Sin (ACFIC).

Ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da hadin kai tsakanin jam'iyyun siyasa da kuma tsarin neman shawarwarin kan harkokin siyasa, karkashin shugabancin jam'iyyar kwaminis, tare kuma da ba da karfin gwiwa ga jam'iyyun siyasa wadanda ba na kwaminis ba, da su dage wajen nuna muhimmancinsu kan harkoki da suka shafi kasar.

A kuma madadin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, Mr. Xi ya taya sabbin shugabannin jam'iyyun guda takwas da kuma na ACFIC murna, tare da mika gaisuwa ga mambobin jam'iyyun, da na ACFIC.

A karkashin tsarin hadin kai tsakanin jam'iyyu na kasar Sin, jam'iyyun siyasa wadanda ba na kwaminis ba, da ita jam'iyyar kwaminis din kanta, suna aiki tare, da kuma sa ido a kan juna.

Ya zuwa ranar juma'a, daukacin jam'iyyun guda takwas sun gabatar da manyan tarukansu suka kuma zabi sabbin kwamitocin tsakiya, wato bayan da jam'iyyar kwaminis ta kasar sin tayi nata sauyin shugabannin a cikin watan nuwamba.

Yayin tattaunawa da shugabannin jam'iyyun, Mr. Xi ya saurari shawarwarinsu a kan muhimman batutuwan da suka hada da inganta tsarin aiki, kara zammar sauye-sauye na tattalim arziki da kuma bunkasa sauye-sauye a fannin kiwon lafiya.

Ya zuwa karshen shekara ta 2011, jam'iyyun guda takwas suna da mambobi sama da dubu dari takwas, wadanda akasarinsu kwararru ne da masu karatu, daga fannoni dabam dabam, Sinawa a kasashen waje da suka dawo kasar Sin, mutane dake da alaka da tsohuwar jam'iyyar Kuomintang(KMT), da kuma mazauna Taiwan.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China