in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
JKS ta tsaida kudurin tafiyar da tsarin karbar takardun shawarwari daga wajen wakilan jam'iyyar don kyautata demokuradiyya
2012-11-11 16:52:27 cri
An gabatar da kudurin tafiyar da tsarin karbar takardun shawarwari daga wajen wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin a cikin rahoton taro na 18 na wakilan jam'iyyar, wanda ya zama muhimmin kudurin da JKS ta tsayar a karon farko a hukunce da ya shafi tsarin samun demokuradiyya a cikin jam'iyyar.

Wu Hui, mataimakin farfesa na jami'ar tsakiya ta JKS ya bayyana cewa, wannan shi ne wani muhimmin mataki na daban da aka tsara don kyautata tsarin babban taron wakilan jam'iyyar, bayan da aka tsaida aiwatar da tsarin wa'adin wakilan taron jam'iyyar a yayin taro na 17 na wakilan jam'iyyar.

Hakan inji Wu Hui shi ya nuna cewa, wakilan taron jam'iyyar za su gabatar da shawarwarinsu kan manufofin jam'iyyar nan gaba bisa tsarin. yana mai ganin cewa, wannan zai ciyar da tsarin samun demokuradiyya a cikin JKS zuwa gaba.

Wang Zhiqiang, wakilin taro na 18 na wakilan JKS kuma daraktan reshen jam'iyyar da ke jami'ar kimiyya da fasaha ta wutar lantarki ya bayyana cewa, tsarin karbar takardun shawarwari daga wajen wakilai yana daya daga cikin hanyoyin da wakilan jam'iyyar ke bi don sauke nauyin da ke wuyansu, wanda zai kara azama gare su wajen gudanar da aiki, da yin nazari kan bukatu da muradun jama'a yadda ya kamata, ta yadda za a iya kyautata matsayin raya jam'iyyar bisa ilmin kimiyya.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China