in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyun siyasa a kasashen Afrika da shugabannin siyasa sun mika sakon taya murna a kan babban taron JKS
2012-11-11 17:43:38 cri
Jam'iyyun siyasa da shugabannin siyasa daga kasashen Afrika suna ta mika sakon taya murna ga kasar Sin dangane da babban taro karo na 18 na JKS wanda aka bude a ranar Alhamis da ta gabata.

Shugaban Liberation Front na kasar Mosambique kuma shugaban kasar Armando Guebuza a sakon taya murna ya jaddada goyon bayansa ga cigaban JKS da kuma al'ummar kasar Sin tare da nuna aniyarsa ta ci gaba da kulla dangantaka mai karko a tsakanin jam'iyyun siyasa, gwamnati da kuma al'ummomin kasashen biyu.

Armando Guebuza ya yi fatan za'a kammala babban taron na JKS cikin nasara, kuma jam'iyyar ta Liberation Front ta Mozambique tana sa ido na ganin an samu hadin kai mai zurfi tare da abokantaka da JKS a kan manufofinsu da suka zo daidai da juna na samar da zaman lafiya, adalci da inganta cigaba da walwala.

A nasa sakon taya murnar, babban magatakardar Rally na al'ummar kasar Togo kuma shugababn kasar Faure Gnassingbe ya ce, babban taron na JKS ana yin shi ne a daidai lokacin da Sin ke bukatar sabbin dabaru da tsare tsaren da za ta fuskanci sauyin da ake fuskanta ta hanyar tattalin arzikin da cigaba al'umma.

Jam'iyyar ta kasar Togo ta yi imanin cewa, sabbin shugabannin kasar Sin da za su fito za su cigaba da zurfafa gyare gyare da inganta rayuwar jama'a tare da kyautata matsayin kasar Sin na wata babbar mai karfin iko a duniya.

Francois Bozize, shugaban farko na jam'iyyar KWA NA KWA na kasar jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya ya ce, a 'yan shekarun nan kasashen biyu sun yi hadin kai sosai a fannin siyaya, tattalin arziki da kasuwanci. Don haka in ji Bozize wanda shi ne shugaban kasar, ya ce kasarsa a shirye take da ta kara hadin kai da kasar Sin don samar da makoma mai haske.

A nasa sakon a madadin Jamhuriyar Niger, ministan harkokin kasashen waje kuma shugaban Jam'iyyar NPD na wucin gadi, Mohammed Bazoun ya ce, JKS a kulluyaumin tsaye take tsayin daka a kan akidarta, abin da ya sa har yau take kan samun nasara da cigaba mai karko. Ya ce, JKS ta maida Sin ta zama wata muhimmiyar kasar da ba za a iya yi ba sai da ita a ko'ina a dandalin duniya, kuma ta zama wata kasa mai amana ta wajen hadin kai da sauran kasashen masu tasowa da suka hada da Jamhuriyar Niger, inji ministan.

Shi ma babban magatakardar Jam'iyyar Patriotic Front ta Ruwanda, Francois Ngarambe ya ce, jam'iyyarsa ta yi farin ciki na ganin babban cigaban da Sinawa suka samu a karkashin jagorancin JKS.

Ya ce, yana mika sakon taya murna tun kafin a kammala babban taron ga sabbin shugabannin da za'a zaba wadanda za su ingiza JKS da al'ummar Sinawa zuwa ga wani babban matsayi na nasara nan gaba. Yana mai cewa, abotan dake gudana a yanzu haka tsakanin kasashen biyu zai cigaba da karfafa.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China