Chao Weidong ya nuna cewa, a yayin da yake ganawa da wasu jami'an kasashen Afirka, ya lura cewa, wasu jam'iyyoyin siyasa da manyan jami'ai na kasashen kudancin Sahara sun mai da hankali sosai kan ayyukan shirinmu kan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 kuma suna fatan za a samu nasarori da dama a cikin taron. Kuma wasu jami'an sun nuna cewa, babban taron nan ya zama wani muhimmin taron wanda zai takaita ayyukan kasar na shekaru 10 da suka gabata, har zai taimaka wajen gudanar da ayyukan kasar na gaba, sun kuma yi imani cewa, sabbin shugabannin Sin za su dukufa matuka wajen kara kyautata zaman rayuwar jama'ar Sin.
Chao Weidong ya bayyana cewa, jam'iyyoyin kasashen Afirka suna mai da hankali sosai kan dangantakar da ke tsakaninsu da jam'iyyar kwaminis ta Sin, suna fatan za a yi musaya ra'ayi mai zurfi tsakanin bangarorin biyu, ta yadda za a iya yin cudanya kan fasahohin da aka samu da kuma fuskantar da kalubaloli don cimma burin ci gaba tare.
Ya kuma nuna cewa, ya zuwa yanzu, an riga an samun sakwannin taya murna daga wasu kasashen Afirka. (Maryam)