Ogwu wadda ta bayyana hakan a jiya Asabar yayin da take tsokaci kan hare-haren baya bayan nan a jihohin Kaduna da Kano, ta ce ta'addanci lamari ne da ya shafi dukkanin sassan duniya, wanda kuma ke bukatar matakan kasa da kasa wajen magance shi.
Kazalika jami'ar ta ce har ya zuwa wannan lokaci, ba a fidda tsammanin kubutar da 'yan matan ba, ana kuma daukar dukkanin matakai domin ganin hakan ta tabbata.
Yanzu haka dai 'yan matan na Chibok sun shafe kwanaki sama da dari a hannun 'yan Boko Haram. Kungiyar da tuni aka sanyawa takunkumin hana mallakar makamai da dakatar da kadarorinta cikin jerin kungiyoyin ta'addanci masu alaka da Al-Qaeda.
Wani bincike da kungiyar "Human Rights Watch" ta fitar, ya nuna cewa cikin watanni 6 na farkon wannan shekara kadai, hare-hare 95 da mayakan kungiyar suka kaddamar sun hallaka mutane sama da 2000. (Saminu)