141015-cpi-zainab.m4a
|
Bisa alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta gabatar, ya nuna cewa, a watan Satumba ma'aunin farashin kayayyaki wato CPI na kasar Sin ya karu da kashi 1.6 cikin dari bisa na watan Agusta, ko da yake karuwar yawansa ta fi sauka a shekarar bana, amma farashin wasu kayayyaki da ayyukan hidima ya ci gaba da karuwa sosai. Alal misali, farashin 'ya'yan itatuwa ya karu da kashi 16.7 cikin dari. A yayin da aka fara harkokin karatu a makarantu, kudin dalibai a makarantun reno ya karu da kashi 5.7 cikin dari, yayin da kudin karatun daliban jami'a ya karu da kashi 3.7 cikin dari. A birnin Beijing, mutane da dama sun bayyana cewa, sun shaida karuwar farashin kaya kadan.
Karuwar alkaluman CPI a watan Satumba ta ragu da kashi 0.4 cikin dari bisa na watan Agusta, amma ta kara raguwa zuwa kasa da kashi 2 cikin dari. Mataimakin shugaban sashen nazari na cibiyar yin mu'amala a fannin tattalin arziki a tsakanin kasa da kasa ta kasar Sin Wang Jun ya bayyana cewa,"Akwai dalilai biyu, na farko shi ne a watan Agusta farashin kayayyakin ya karu yayin da ya ragu sosai a watan Satumba. Na biyu shi ne farashin abinci ya ragu bayan da ya karu kadan a farkon wannan wata. Musamman farashin kwai ya ragu sosai. Amma farashin kaya da bai shafi abinci ba bai karu sosai ba, don haka aka samu saurin karuwar alkaluman CPI a watan Satumba"
Ban da CPI, yawan PPI na kasar Sin a watan Satumba ya ragu da kashi 1.8 cikin dari bisa na watan Agusta, wanda ya ci gaba da raguwa a watanni 31 a jere. Hukumomi da dama na kasar sun yi tsammani cewa, alkaluman PPI na kasar ba zai karu a bana ba. A ganin Wang Jun, raguwar farashin kaya da rashin karuwar tattalin arzikin kasar za su kawo illa ga kokarin da ake na samar da kayayyaki da zuba jari. Wang Jun ya ce,"An samu raguwar alkaluman PPI ne a sakamakon wasu dalilai na cikin gida, ga misali raguwar bunkasuwar tattalin arziki da ake ta fuskanta ta shafi farashin kayayyakin masana'antu. Na biyu shi ne gwamnatin kasar Sin tana kokarin daidaita da kuma rage yawan kayayyakin da suka wuce kima da masana'antu suka samar, wanda ya kawo illa ga kokarin da ake na zuba jari. A sakamakon raguwar farashin kayayyaki, za a fuskanci yanayin kasuwa maras tabbas wajen fitar da kayayyaki."
Bayanai na nuna cewa, an fi samun raguwar alkaluman PPI na kasar a watan Satumba, sakamakon raguwar farashin man fetur da karafa. Kana raguwar farashin muhimman kayayyaki da aka samu a kasashen duniya ta shafi farashin kayayyakin da masana'antu ke samarwa sosai. Wang Jun ya yi hasashe cewa, sakamakon raguwar farashin kayayyaki musamman koma bayan alkaluman PPI, babbar matsalar da tattalin arzikin kasar Sin zai fuskanta ita ce biyan bukatu amma ba saurin karuwar farashin kaya ba.(Zainab)