Mr. Gong Xiaosheng, wakilin musamman na kasar Sin kan batun yankin Gabas ta Tsakiya ya yi wannan furuci ne a yayin taron kasa da kasa na sake gina yankin Gaza da aka yi a birnin Alkahira na Masar a ran 12 ga wata.
A yayin da ya bayar da jawabi, Mr. Gong Xiaosheng ya nuna cewa, rikicin da aka shafe kwanaki 50 ana yinsa a yankin Gaza ya haddasa mutuwa da raunukan dimbin mutane da hasarar dukiyoyi masu tarin yawa, har ma fararen hula da dama sun gudu daga gidajensu. Wannan lamari ya bata ran bangaren Sin sosai. A ganin bangaren Sin, nauyin sake gina yankin Gaza mafi muhimmanci da aka dora wa bangarori daban daban shi ne bangarorin Palesdinu da Isra'ila su aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da suka kulla a birnin Alkahira, kuma su hanzarta yin shawarwari kan yadda za a iya tsagaita bude wuta har abada a tsakaninsu. Bugu da kari, ya kamata bangarorin Palesdinu da Isra'ila su hanzarta farfadowa da kuma ingiza yin shawarwari kan batun shimfida zaman lafiya tsakaninsu, ta yadda za a iya tabbatar da sauke nauyin sake gina yankin Gaza. Don haka, ya kamata gamayyar kasa da kasa ta samar da karin taimako, kuma ta aiwatar da kuduran M.D.D. da abin ya shafa domin nuna goyon baya mai karfi ga kokarin yin shawarwarin kawo zaman lafiya a siyasance.
Bisa wani labari daban da aka bayar, an ce, a ran 12 ga wata a birnin Alkahira na Masar, ministan harkokin wajen kasar Norway Borge Brende ya yi shelar cewa, a yayin taron kasa da kasa na sake gina yankin Gaza, kasashen duniya sun alkawarta cewa, za su samar da kudin tallafi na dalar Amurka biliyan 5.4 ga kokarin raya tattalin arzikin Palesdinu da sake gina yankin Gaza. (Sanusi Chen)