in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faransa ta fara daukar matakai a CAR
2013-12-07 17:18:36 cri
Wata sabuwa kuma, Ministan tsaron kasar Faransa Jean-Yves Le Drian ya bayyana a ranar 6 ga wata cewa, ta fara daukar matakan soji a jamhuriyyar Afirka ta Tsakiya don sa kaimi ga farfado da zaman lafiya a kasar.

Jean-Yves Le Drian ya bayyana wa 'yan jarida na kasar Faransan cewa, mai yiwuwa ne sojojin kasar Faransan su yi aiki a jamhuriyyar Afirka ta tsakiya har tsawon watanni shida, kuma makasudin aikin nasu shi ne farfado da zaman lafiya a kasar da kuma taimakawa wajen jibge sojojin kasashen Afirka a kasar. Kana ya ce, wani rukunin sojojin Faransan da ya tashi daga kasar Gabon ya riga ya isa jamhuriyyar Afirka ta tsakiya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China