140314murtala
|
Gwamnan jihar Jigawa dake arewacin Najeriya, Alhaji Sule Lamido, ya sanar da cewa gwamnatin jihar za ta bada gudunmawar naira miliyan 13 a shirye-shiryen gudanar da biki da laccar tunawa da ranar Malam Aminu Kano ta wannan shekarar da za a gudanar a jihar Kano.
Gwamna Sule Lamido ya bayyana hakan ne yayin da hukumar gudanarwar Gidan Mambayya, karkashin jagorancin Farfesa Muhammad Suleiman suka ziyarce shi a ofishin sa dake garin Dutse.
Gwamnan ya ce Malam Aminu Kano na da matukar muhimmanci a tarihin siyasar kasar nan, saboda irin gwagwarmayar da yayi a wurin kwato 'yancin talakawan kasar nan. Ya ce Koyarwa da sadaukarwar da marigayi Malam Aminu Kano ya yi don kwatowa talakawa 'yancin su, ya kamata kowa ya yi koyi da hakan. A don haka in ji shi gwamnatin jihar Jigawa a koda yaushe a shirye take ta fito da irin wannan kokari don tunawa da wannan dan kishin kasa.
A nasa jawabin Farfesa Suleiman ya godewa gwamna Lamido sakamakon wannan namijin kokarin da yayi.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.