in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yayin da zaben 2015 ke kara karatowa, a jihar Kano dake arewacin Najeriya masu neman  gadar Injinya  Rabi`u Musa Kwankwaso sun fara karaya sakamakon wasu kalamai da yayi.
2014-03-22 15:43:06 cri

A tarayyar Najeriya yanzu haka kasuwar bukata ta fara ci sakamakon karatowar babban Zaben kasar a shekara ta 2015.

Irin wannan kasuwa ta bukata ta fara kankama ne a matakan jahohi da kananan hukumomi da kuma tarayya.

Tun dai a farko wannan shekarar ce `yan siyasa a dukkan matakai a tarayar Najeriya suka fara tuntubar magoya bayan su game da yadda za a tunkari zaben 2015.

Wasun su ma sun fara bazama mazabu domin yin tozali da masu kada kuri` a da nufin samun Karin goyon bayan yin tazarce, ko kuma neman izinin jama`a da shugabannin jam`iyya domin samun damar tsayar dasu takara.

A jihar Kano , kashi 80 na `yan majalissar wakilai data Dattawa da kuma `yan majalissar dokoki ta jiha suna da muradin sake tsayawa, yayin da aka samu karuwar sabbin mabukata wayannan mukamai.

Ko da yake dunkulewar jam`iyyun adawa na taka rawa ga haduwar kawunan jama`a a babban zaben mai zuwa, amma babu tabbas na hasashen jam`iyyar da zata taka rawar azo a gani yayin zabukan anan Kano bisa la`akari da yadda manyan jam`iyyun APC da PDP suka mike tsaye wajen yada manufa da farautar magoya baya.

Kowacce jam`iyya dai daga cikin wadannan jam`iyyu biyu suna alfahari da karfin gwamnati, jam`iyyar APC na alfaharin itace keda jagorancin jihar Kano, yayin da kuma jam`iyyar PDP na alfaharin tana da sama watto tarayya.

Kasancewar watanni biyu kacal ya rage a gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar, a halin yanzu hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano ta himmatu wajen shirye shiryen gudanar da zaben, a inda ta ke cigaba da horas da ma`aikata da kuma wayar da kan jama` a game da yadda zaben zai kasance da kuma ka`idojin zaben.

Yayin da su kuma shugabannin jam`iyya suna ta gudanar da tarukan sulhu ga `yan takarar mukaman shugabannin kananan hukumomi da kansiloli domin tabbatar da ganin an yiwa kowanne dan takara adalci.

A ranar asabar din nan ne dai ake sa ran shugabannin jam`iyyar APC na kananan hukumomi zasu gabatar da cikakkun sunayen yan takarar kansilolin, yayin da kuma jam`iyyar PDP ta ke shirin gudanar da zaben fidda `yan takara a yankunan da aka gaza yin sulhu tsakanin `yan takara.

Sai dai kuma wani abu da yake neman tayar da rudani a tsakanin `yan jam`iyyar APC a jihar ta Kano shi ne kalaman da gwamnan jihar Injiniya Rabi`u Musa Kwankwaso yayi a kwanan nan inda yake cewa sai wanda yake sanya jar hula ne kawai zai gaje shi, wato dai anan duk wanda ya fito daga tsoffin jam`iyyun ANPP da CPC kada ma ya nemi bukatar takarar gwamna.

A halin yanzu akwai mutane biyu da basa saka jar hula kuma suna da muradin tsayawa takarar gwamna, irin su Hon Abdulrahman Kawu Sumaila mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalissar wakilai ta tarayya da kuma Sanata Kabiru Gaya.Babu shakka kalaman sun sanyaya gwiwar masu neman gadar gwamnan, koda yake har yanzu babu daya daga cikin su daya yi Magana da `yan jaridu akan wannan batu.

Haka kuma gwamnan yace matashi zai baiwa damar gadar sa, amma ba mai yawan shekaru ba, alhalin kuwa mataimakin sa Dr. Abdullahi Umar Ganduje mai shekaru 68 yana mutukar sha`awar ya gaji mukamin gwamnan.

Babu shakka kalaman da gwamna Rabi`u Musa Kwankwaso yayi ya sanyaya gwiwar masu bukatar tsayawa takarar gwamnan jihar Kano a shekarar badi.

A wannan rana ta asabar ce ake sa ran dawowar gwamnan na Kano daga kasar Amurka inda yaje ziyarar aiki, kuma mai yiwuwa ne ya warware wannan takaddama idan ya dawo.

Koma dai me ake cikin, zaben 2015 a Najeriya zai zo da wani sabon salo, kuma zai nuna karfin yanci na masu kada kuri`a bisa la`akari da irin burin da `yan Najeriya suka ci na neman kawo sauyi mai ma `ana da zai fitar da kasar daga kangin fitintinun addini dana kabilanci, rashin aikin yi da kuma talauci(Garba Abdullahi Bagwai)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China