A jawabinsa ministan ya ce, bana ita ce zagayowar shekara ta 100 bayan barkewar babban yakin duniya na farko, kana shekara mai zuwa za ta kasance cikowar shekaru 70 bayan kammalar babban yakin duniya na 2. A wannan lokaci, in ji ministan, ya kamata kasashe daban daban su yi kallon juna cikin daidaituwa, sa'an nan su tsaya kan bin dokoki da nuna adalci don neman samun zama lafiya da ci gaban al'umma.
Dangane da batun Sudan ta Kudu, mista Wang ya ce, kamata ya yi bangarorin 2 dake rikici da juna su tsagaita bude wuta nan take, don gudanar da shawarwari, ta yadda za su cimma matsaya tare da tabbatar da hanyar da za a bi don daidaita matsalar kasar, bisa kokarin shiga tsakani da kungiyar raya gabashin Afirka ta IGAD take yi.
Sa'an nan game da batun Ukraine, Wang Yi ya ce, kasar Sin na fatan ganin MDD ta taka rawar da ta kamata don daidaita maganar kasar, kana tana goyon bayan gamayyar kasa da kasa kan kokarinta na sassanta yanayin da ake ciki a gabashin kasar a fannin aikin jin kai.
Haka zalika, yayin da Wang ya tabo maganar Syria, ya ce an yi shekaru 4 ana ta samun yake-yake a kasar, a ganin kasar Sin, shawarwari, maimakon fada,shi ne zai sa a samu hanyar mafita.
Sa'an nan dangane da batun yaki da ta'addanci, Wang ya ce, kasar Sin ta ki amincewa da ko wane nau'in ayyukan ta'addanci. Ya jaddada cewa, bai kamata ba a bi ma'auni 2 wajen yaki da ta'addanci, kana kada a alakanta ta'adanci da wasu kabilu ko kuma wani addini.
Har wa yau kuma, Wang Yi ya bayyana ra'ayin kasar Sin kan wasu batutuwan da suka shafi Iraki, Palesdinu, Afghanistan, maganar nukiliya a kasashen Iran da Koriya ta Arewa,da kuma batun sauyin yanayi, shirin raya kasa a bayan shekarar 2015, da dai makamantansu. (Bello Wang)