murtala0805.m4a
|
Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin gwamnan jihar Alhaji Dr Ibrahim Gaidam ta bakin kakakinsa Alhaji Abdullahi Bego a jawabinsa dangane da yadda 'yan bindigar suka rika kai hare-hare babu kakkautawa a wasu sassan jihar Yobe, inda har suka kai hare-haren boma-bomai akan wasu al'ummomin yayin da suke gudanar da sallah a cikin garin Potiskum, hare-haren da suka yi sanadiyyar rayukan mutane kusan 12 tare da jikkata mutane masu yawan gaske, bayan harin da suka kai a garuruwan Katarko, Gujba da kuma Buni Yadi.
Gwamna Gaidam ya kara da cewar wadannan hare-haren da 'yan bindigar suke kaiwa al'ummomin da ba su ji ba ba su gani ba, sam-sam ba musulunci ba ne, hasali ma masu aikata hakan sun yi hannun riga da musulunci.
Don haka gwamnan ya yi matukar nuna kaduwarsa dangane da wannan irin aika-aika, ya kuma jajantawa al'ummomin da wadannan hare-hare suka rutsa da su, dangane da hakan ne ya bada umarni ga hukumomin asibitocin da aka kwantar da mutanen da suka ji munanan raunukan da su baiwa dukkannin mutanen magani da jiyya kyauta, har zuwa lokacin da Allah zai kawo musu sauki.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.