in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an Korea ta kudu da na Amurka sun tattauna a kan batun DPRK a Seoul
2014-10-06 16:57:02 cri
Wasu kusoshin gwamnatin Amurka wadanda suka ziyarci Seoul sun tattauna da takwarorinsu na Korea ta kudu a kan batutuwan da suka shafi jamhuriyar damokradiyyar jama'ar Korea DPRK a yau Litinin bayan wata babbar ziyarar ba zata da jami'an Korea ta Arewa suka kai Korea ta Kudu a ranar Asabar da ta gabata.

Mataimakin sakataren ma'aikatar harkokin wajen Amurtka Daniel Russel da kuma mataimakin mukaddashin sakataren harkokin tsaro na kasar ta Amurka David Shear sun isa birnin Seoul ne a ranar Lahadi a ranar Litinin, kuma suka gana da mataimakin ministan harkokin waje na bangaren siyasa na Korea ta kudu, Lee Kyung-soo a babbaar hedkwtar ma'aikatar harkokin wajen kasar.

Ziyarar jami'an ta biyo bayan ziyarar mataimakin kwamandar kasar Korea ta arewa Hwang Pyong So wanda ya kai Korea ta kudu wata ziyarar ba zata a ranar Asabar a yayin bukin kammala wasannin motsa jiki na kasashen Asia.

Russel ya shaidawa 'yan jarida a karshen taron cewar Amurka na goyon bayan fafutukar Korea ta Kudu a bangaren na karfafa dankon zumunci tsakanin cikin gida da na wajen kasar. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China