Yayin zantawar ta su, Mr. Li ya isar da sakon fatan murna da alherin shugaba Xi Jinping na nan kasar Sin ga Mr. Zuma. Ya na mai cewa kasar Sin na fatan kara amincewa r juna bisa manyan tsare tsare, tsakanin ta da Afirka ta Kudu. Baya ga batun zurfafa mu'amala, da sada zumunci, da hadin gwiwa a dukkanin fannoni, duka dai da nufin karfafa dangantakar abokantaka, bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni tsakanin kasashen biyu.
A nasa bangare, shugaba Zuma ya godewa shugaba Xi bisa zumunci, na tura manzon musamman domin halartar bikin rantsuwar sa. Yana mai fatan Mr. Li ya isar da gaisuwarsa ga shugaba Xi.
Kaza lika Zuma ya jaddada muhimmancin nagartar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa kasar sa, na fatan kiyaye moriyar kasashen, da ma ta sauran kasashe masu tasowa tare da Sin, a kokarin da ake yi na kafa zamantakewar duniya mai cike da adalci.(Fatima)