A jiya Lahadi ne, shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya nada Cyril Ramaphosa a matsayin mataimakinsa, tare da bayyana sunayen mutanen da ke cikin sabuwar majalisar ministocin kasar.
Zuma ya shirya wani taron manema labaru a ran nan a birnin Pretoria, inda ya tabbatar da samun mataimakinsa da sunayen 'yan sabuwar majalisar ministoci, tare da sanar da kafa sababbin ma'aikatu wato ma'aikatar sadarwa da ba da hidimar aikewa da wasiku, da ma'aikatar albarkatun ruwa da kiwon lafiya, da ma'aikatar raya kananan masana'antu.
A cikin sabuwar majalisar ministoci, akwai ministoci 35, wadanda suka hada da Nhlanhla Nene a matsayin ministan kudi, da Maite Nkoana-Mashabane wanda zai ci gaba da zama ministan raya dangantakar kasashen waje da hadin kai, sai Nosiviwe Mapisa-Nqakula wanda ya zama ministan harkokin tsaro da sojojin masu ritaya, yayin da kuma Rob Davies zai ci gaba da zama ministan cinikayya da masana'antu. (Danladi)