in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta tabbatar da samun mai dauke da ebola a karo na farko a kasarta
2014-10-01 16:37:53 cri
Amurka a ranar talatan nan ta tabbatar da cewa a karo na farko kasar ta samu mai dauke da cutar ebola a Dallas na jihar Texas.

Da yake tabbatar da hakan Tom Frieden babban directa a cibiyar shawo kan cututtuka da kariya yace mara lafiyar da ake kula dashi a asibitin Texas ya nuna cewa yana dauke da cutar babu tantama, wadda ake dauka ta hanyar shafar wani ruwan jikin mai dauke da cutar kamar jini da fitsari a cewar talabijin din jihar ABC13.

Mara lafiyan wanda ya bar kasar Liberiya a ranar 10 ga watan satumbar nan data kare ya isa kasar Amurka ne a ranar 20 ga watan satumbar sannan ya nemi taimakon asibiti a ranar 27 ga watan na satumba kuma kashe garin ranar aka killace shi don lura da lafiyarsa, inji Frieden.

Sai dai Darektan yana da tabbacin cewa ba za a samu barkewar cutar a kasar ba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China