Banbury ya fadi hakan ne a ganawar da yayi da manema labarai bayan isarsa Ghana dake yammacin Afrika yana mai cewa barkewar cutar Ebola ya fi karfin rikici a lafiyar al'umma.
Babban jami'in yayi nuni da cewa yanayin da cutar ebola ta haifar yayi kamari kuma ya shafi ko wane bangare a fannin tattalin arziki, zamantakewa da tsaro. Ya bayyana cewa adadin yaduwar cutar yawan wadanda suka rasa rayukan su a cikin fiye da watannin 6 da barkewar ta yafi karfin yadda ake zato ya koma kamar wani abin almara sannan kuma abu ne da ba za'a iya kayyade adadin a nan gaba ba.
Anthony Burbury yace duniya yanzu ta amince cewar hadarin da kasashe uku ke ciki zai iya shafar yankunan baki daya da ma nahiyar gaba daya har ma da duniya illahirin ta abin da kuma zai shafi tsaro da zaman lafiyar kasa da kasa. Babban jami'an daga nan sai yayi nuni da cewa akwai bukatar hada karfi daga dukkan kasashen duniya don ganin an shawo kan wannan annoba da hana yaduwar ta.