Domin cimma burin gudanar da aikin hajji lami lafiya, gwamnatin kasar Saudiyya ta kafa wani rukunin musamman dake kunshe da sojoji dubu 40, kuma ta tura jami'an tsaro fiye da dubu 90 domin su kula da harkokin tsaro lokacin aikin hajji a Mekka. Ban da wannan kuma, don magance abkuwar hadari, gwamnatin kasar ta ajiye na'urorin bidiyon sa ido guda 32a cibiyar kula da tsaron jama'a a wurin Hajji. Idan hadari ya faru, jami'an tsaro za su iya isar wurin ba tare da bata lokaci ba. (Zainab)