in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jirgin saman shata dake dauke da wani rukuni na mahajattan kasar Sin ya tashi zuwa kasar Saudiya
2013-09-18 16:57:01 cri
A ranar Talata 17 ga wata ne, jirgin saman shata na farko na kamfanin China Southern na kasar Sin dake dauke da mahajattan kasar ya tashi daga birnin Urumqi na jihar Xinjiang zuwa kasar Saudiya.

An ce, musulman kasar Sin da za su je Makka don yin hajji na bana sun wuce dubu 11.8, kamfanonin jiragen sama na China Southern, China East, da Air China ne za su aika da jiragen sama 38 don jigilar maniyyatan daga biranen Urumqi, Lanzhou, Yinchuan, Kunming da kuma Beijing zuwa Madina.

A matsayinsa na babban kamfanin dake daukar nauyin jigilar maniyyatan, kamfanin China Southern, zai aika da jiragen sama da jimilarsu za ta kai 20 don kammala aikin, yawan mutanen da za a yi jigilarsu za su kai 6840.

Shugabannin reshen kamfanin China Southern na kasar Sin dake jihar Xinjiang sun mayar da hankali sosai kan wannan aiki, har ma sun kira tarurruka da dama, don ba da tabbacin gudanar da aikin na bana yadda ya kamata. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China