in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kulaf din kwallon kafar Zambia ajin mata zai kara da na Kamaru a wasan sada zumunta
2014-08-20 16:56:55 cri
Rahotanni daga kasar Zambia na cewa kungiyar kwallon kafar kasar ta mata mai suna Chipolopolo, za ta buga wasannin sada zumunta 2 da takwarar ta ta kasar Kamaru, a wani shiri na share fagen tunkarar gasar cin kofin nahiyar Afirka ajin mata, wanda za a buga nan gaba cikin wannan shekara.

Hakan dai a cewar hukumar kwallon kafar kasar ta Zambia ya biyo bayan amincewar da takwarar ta su ta Kamaru ta yi, ta bude sansanin horas da 'yan wasan a kasar ta Zambia har ya zuwa lokacin gasar cin kofin na Afirka da za a gudanar a kasar Namibia cikin watan Oktoba mai zuwa.

Da yake karin haske game da wannan batu, wani mai magana da yawun hukumar kwallon kafar kasar ta Zambia FAZ, ya ce nan gaba kadan za a sanar da lokacin buga wadannan wasanni 2. Kakakin na FAZ ya kuma kara da cewa baya ga Chipolopolo, kulaf din na kasar Kamaru zai buga wasu wasannin na daban, da wasu karin kulaflikan mata dake kasar ta Zambia.

Tuni dai 'yan wasan na Chipolopolo suka matsa kaimi wajen atisaye, gabanin gasar cin kofin na Afirka dake tafe, inda za su kara da Namibia da Kwadebuwa da Najeriya a gasar wadda Namibia za ta karbi bakunci.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China