Bisa gayyatar da gwamnatin kasar Sin ta yi masa, mista Ban zai kawo wa kasar Sin ziyarar aiki daga ranar 18 zuwa 21 ga wata. A lokacin da yake zantawa da manema labaru kafin ya tashi zuwa kasar Sin, mista Ban ya bayyana cewa, akwai huldar abokantaka mai danko a tsakanin kasar Sin da MDD. Ya ce, kasar Sin na daya daga cikin muhimman kasashe mambobin MDD. Kuma sakamakon bunkasuwar tattalin arzikinta ya sa kasar Sin kara yin tasiri a duk fadin duniya. Mista Ban yana fatan kasar Sin za ta kara ba da gudummawa a duniya wajen kiyaye zaman lafiya da kara azama kan samun ci gaba mai dorewa.
Har wa yau kuma, mista Ban ya ce, a lokacin ziyararsa a kasar Sin, zai yi shawarwari da shugabannin kasar dangane da wasu muhimman al'amuran kasa da kasa da na shiyya-shiyya. Kana kuma zai yi musayar ra'ayoyi da shugabannin kasar Sin game da batun samun dawamammen ci gaba.(Tasallah)