Wasu takardun bayan taron da aka fitar sun bayyana bukatar da majalisar kasashen Turai ta gabatar ga kwamitin kungiyar EU game da kara kwazo, ta yadda za a kai ga cimma wasu shawarwari cikin makon dake tafe, duka dai da nufin kaiwa ga daukar karin matakai kan kasar ta Rasha game da halin da ake ciki a kasar Ukraine.
Shugaban majalisar Turai Herman Van Rompuy, ya ce yanayin da ake ciki a Ukraine a kwanaki 3 da suka gabata ya yi matukar tsananta, don haka ake bukatar mai da hankali sosai kan kokarin dakatar da zub da jini, da magance kara tsanantar yanayin. Har ila yau ya ce takunkumin da kungiyar EU ta kakabawa Rasha a karshen watan Yulin da ya gabata, ya yi matukar tasiri ga tattalin arzikin ta.
Shi kuwa a nasa bangare, shugaban kwamitin kungiyar EU Jose Barroso, cewa ya yi sanya takunkumin ba shi ne babban burin da aka sanya gaba ba, sai dai ya zama wabiji ne kawai a kakaba shi, domin tilasawa Rashan fahimtar kuskurenta.
Haka zalika Barroso ya jaddada cewa, daukar matakan soji ba za su taba warware matsalar Ukraine ba, don haka ya bukaci Rasha da ta yi hadin gwiwa da kungiyar EU da ma kasar Ukraine a kokarin da ake yi na wanzar da zaman lafiya da lumana a kasar. (Bello Wang)