Gwamntin kasar tana nazari kan wannan batu, akwai abubuwa maras kyau koda an dubi wannan matsala gaba daya, akwai alheri da dama fiye da matsalolin dake cikin takunkumin, in ji shugaba Putin a gaban 'yan jarida bayan dandalin kungiyar hada kai ta Shanghai SCO a Douchanbe.
Shugaban Rasha ya nuna ko in kula game da wadannan sabbin takunkumin na kungiyar tarayyar Turai (EU), tare bayyana cewa "ina yabo da wannan mataki na kungiyar EU, domin kuwa wakilanmu da shugabannin kamfanoninmu na balaguro a kasashen waje da tattauna harkoki na yanzu, hakan ma ya fi, a wani labarin da kamfanin dillancin labarai na Interfax ya rawaito. Takunkumin EU na baya bayan nan sun hanawa wasu manyan kamfanonin man fetur uku na Rasha da kuma wasu kamfanoni uku a bangaren tsaro neman kwangiloli a kasuwar tarayyar Turai. Haka kuma takunkumin tarayyar Turai din ya shafi wasu mutanen Rasha 24, wadanda suka hada da 'yan majalisa, a cikin mutanen da aka hana yin tafiya zuwa Turai da kuma rike kudinsu a kasashen waje. Kasar Amurka ita ma ta bayyana sabbin takunkumin dake shafar manyan kamfanonin kasar Rasha. (Maman Ada)