Wata tawagar kwararru ta farko a karkashin shirin MDD na daukar matakin gagggawa a kan cutar Ebola ta isa birnin Accra na kasar Ghana, domin kafa hedkwatarsa a can.
Kakakin MDD, Stephane Dujarric ya bayyana wa manema labarai cewar, Wata tawagar ta dabam ta MDD mai kula da matsalolin da suka shafi kiwon lafiya ita ma ta isa kasar Liberia, wacce ita ce kasa mafi yawan mutane wadanda suka kamu da cutar Ebola.
Kakakin MDD, ya kuma ce, MDD ta kafa wani asusu na hadin gwiwa domin samun gudumuwa daga kasashe a kokarin da ake na tunkarar cutar Ebola. (Suwaiba)