A jawabin sa yayin bude taron shugaban majalisar mista Zhang Dejiang ya bayyana cewa, kamata ya yi a nazarci jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a baya, yayin bikin cika shekaru 60 da kafuwar majalisar, sa'an nan a tsaya kan hanyar gurguzu mai salon musamman ta kasar Sin, da kokarin kyautata tsarin majalisar ta wakilan jama'ar kasar Sin, ta yadda za a samu damar sanya tsarin ya yi cikakken amfani wajen tabbatar da tsarin dimokuradiyya irin na gurguzu a nan kasar Sin.
A cewar mista Zhang, tsarin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na da alaka sosai da kokarin da jam'iyyar Kwaminis ta kasar, da jama'ar kasar suka yi ta fuskar raya kasa, don haka tsarin ke da muhimmanci da amfani matuka.
Ya ce a nan gaba yayin da ake kokarin raya tsarin gurguzu irin na musamman na kasar Sin, da neman cika burin kasar na bunkasa rayuwar al'umma, kamata ya yi a nace ga bin tsarin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, tare da ci gaba da kokarin kyautata shi.(Bello Wang)