A jawabin da ya yi na maraba, shugaba Yameen ya bayyana cewa wannan ziyara da shugaba Xi ke yi, ita ce irinta ta farko da wani shugaban kasar Sin zai gudanar a kasar ta Maldives, tun bayan kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu shekaru 42 da suka gabata. Wanda hakan ya sanya jama'ar kasarsa mai da hankali matuka kan wannan ziyara.
A nasa bangaren, shugaba Xi ya nuna gaisuwa, tare da fatan alheri ga jama'ar kasar Maldives. Ya kuma ce cikin shekaru 42 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Maldives, dangantakar dake tsakanin suna samun bunkasuwa yadda ya kamata, lamarin da ya zama abin koyi ga kasashe kanana da manya, a fannin bunkasa zaman daidaito, da zaman tare cikin lumana.
Shugaba Xi ya kara da cewa, a kwanan baya shugaba Yameen ya kai ziyara birnin Nanjing na kasar Sin, inda ya halarci gasar wasannin Olympic ta matasa na yanayin zafi karo na biyu, wanda hakan ya nuna goyon bayan da gwamnatin sake nunawa ga jama'ar kasar Sin.
Ya ce kasar Maldives muhimmin zango ne a tsohuwar hanyar siliki ta teku, saboda haka ne tun fil azal take da alaka sosai da kasar Sin. Bugu da kari shugaba Xi ya ce kasar Sin na maraba da Maldives, a fannin shiga ayyukan gina hanyar siliki ta teku a wannan karni na 21. Kana tana kuma fatan hada kai da Maldives da nufin fuskantar kalubale tare, da karfafa sada zumunci na gargajiya, da kuma zurfafa hadin kai irin wanda zai haifar da cimma moriyar juna, ta yadda za a iya tabbatar da samun bunkasuwa tare. (Bilkisu)