in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jacob Mulenga ya sauya sheka zuwa Adana Demispor na Turkiyya
2014-08-20 16:56:04 cri
Dan wasan gaban kasar Zambia Jacob Mulenga ya amince da komawa kulaf din kasar Turkiyya mai suna Adana Demispor, bayan da ya ki yarda ya sake sabunta kwantiragin sa da kulaf din FC Utrecht na kasar Netherlands.

Mulenga dan shekaru 30 da haihuwa zai bugawa sabon kulaf din na sa wasa na tsahon shekara guda, kamar dai yadda jaridar Zambia Daily Mail ta rawaito.

Duk kuma da raunukan da ya sha fama da su tsahon shekaru 5 da ya kasance a kulaf din na FC Utrecht, Mulenga ya ciwa kungiyar kwallaye 45 a wasanni 112.

Kafin hakan dan wasan gaban na Zambia ya taba bugawa Strasbourg na kasar Faransa wasa a kakar 2007 zuwa 2008, lokacin da kulaf din sa na wancan zamani Berrichonne Chateauroux ya ba da shi aro.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China