0307murtala
|
Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Gaidam, a yayin da yake kaddamar da hanyar motar da ta tashi daga garin Damaturu zuwa Buni-Gari, ta nufi garin Magza dake da iyaka da jihar Borno mai tsawon kilomita 77, wanda kamfanin RRC zai gudanar cikin shekaru Biyu.
Alhaji Ibrahim Gaidam ya ci gaba da cewa ita wannan hanya duk da cewa hanya ce ta gwamnatin tarayya, saboda matukar muhimmancin da take da shi ga al'ummar jihar, da ma kasa baki daya, ya zama wajibi jihar ta sake gina ta, ba tare da la'akari da nauyin gina ta dake wuyan gwamnatin tarayya.
Ya ce gwamnatin tarayya ta yi watsi da wannan hanya ita wadda tun a farkon shekarun 1970 aka gina ta, amma har zuwa yau ba a taba sa ko da tubali daya a kan ta ba, balle ma tunanin sake gina ta dungurungum.
Gwamnan ya kara da cewa, kowa ya san irin azabar da al'ummomin da ke amfani da wannan hanya ke sha, wadda ganin hakan ne gwamnatinsa ta yanke shawarar gina bangaren hanyar da ke a cikin jihar, don sauke nauyin dake kanta na tallafawa al'ummarta, kasancewar a kullum su al'ummarsu ne a gabansu, ba wai tara kudade da nufin biyan bukatun kai ba.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.