Rundunar hadin-gwiwar sojojin kiyaye zaman lafiya wato JTF dake jihar Yobe a Najeriya ta sanar da kafa dokar-hana-fita na tsawon sa'o'i 24 a karamar hukumar Potiskum, wanda ya fara aiki tun daga ranar Litinin 5 ga wata.
A cikin wata sanarwar da kakakin rundunar JTF dake Yobe Mista Eli-Lazarus ya bayar, ya bukaci mazauna wannan yanki da su nuna hakuri da bada cikakken hadin-kai ga jami'an tsaro, su kuma zauna a gidajen su kada su fito. Lazarus ya yi gargadin cewa kada mazauna karamar hukumar Potiskum su fito daga gidajensu har sai an dage wannan dokar.
Lazarus ya ce, jami'an tsaro na JTF suna fatan jama'a za su ci gaba da ba su bayanai a kan abubuwan da suke da shakku a kai a unguwanninsu, da kara mara musu baya a fannin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Jihar Yobe dai na daya daga cikin jihohi uku da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kakabawa dokar-ta-baci a watan Mayu.(Murtala)