131002-sharhi-yaya
|
A kwanakin baya ne wasu 'yan bindiga a Najeriya,suka dakile mafarkin wasu dalibai a kwalejin koyon aikin gona da ke garin Gujba a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin kasar na samu ilimi,inda suka kai musu hari da dare bayan da gwamnatin jihar ta sake bude makarantu a yankin kwanaki 13 da suka gabata.
A ranar Lahadi da safe ne wasu da ake zaton 'yan kungiyar nan ta Boko Haram suka kai mummunan hari a kwalejin koyon aikin gona da ke garin na Gujba a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya,yayin da daliban ke barci,lamarin da ya sanya hankalin duniya karkata ga kasar da ke da yawan al'umma a nahiyar Afirka.
Masu aikin ceto sun kidaya gawawwaki 47,kana majiyoyin asibiti na bayyana cewa,sun samu gawawwaki 40,kuma har yanzu babu wasu alkaluma a hukumance da ke bayyana adadin wadanda suka mutu sanadiyar lamarin. Sai dai a cewar wadanda lamarin ya faru a kan idonsu, maharan sun yi harbin kan mai uwa da wabi ne a sassa dabam-dabam,kana suka kinnawa azuzuwa da dakuna kwanan dalibai wuta,lamarin da ya kai ga dazuka kamawa da wuta.
A sanarwar da kakakin soja da ke jihar Yobe Laftana Eli Lazarus ya bayar wanda Xinhua ya samu kwafi, ya ki ya yi karin bayani game da wadanda suka mutu. Amma ya ce 'yan ta'addan sun kewaye dakunan kwanan daliban ne,kana suka rika bude wuta ta ko'ina,lamarin da ya haddasa mutuwar daliban tare da jikkata wasu,kana suka yi awun gaba da motar daukar marasa lafiya ta makarantar.
Wani ma'aikacin kwalejin mai suna Ali Mohammed, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ta wayar tarho cewa,hawaye ya cika idanun mutane da dama da suka ziyarci makarantar ranar Lahadi da yamma,yayin da suka ga gawawwakin dalibai da dama kwance a filin Allah-Ta'ala.
Ya ce wasu jami'an gwamnati da suka kai ziyarar ta'aziya kwalejin,sun bayyana takaicin su game da wannan danyen aikin,inda ya ce ana shirin yi wa daliban da suka mutu ne jana'izar gama gari,yayin da aka garzaya da galibin daliban da suka jikkata zuwa asibitin jihar Damaturu domin yi musu magani.
Yayin da ya ke tsokaci a shafinsa na sada zumunta na facebook,Wani Sanata a Najeriya mai suna Abubakar Bukola Saraki,ya bayyana jimaminsa ne game da harin da ya hallaka dalibai sama da 40 a kwalejin koyon aikin gona da ke garin Gujba a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin tarayyar Najeriya.
Ya ce, wannan ba rana ce ta dora laifi ko nuna yatsa ga wani ba ne,amma rana ce ta daukar matakan da suka dace don ganin an zakulo wadanda suka aikata wannan mummunan al'amari ta yadda za a gurfanar da su a gaban kuliya kana a baiwa hukumomin tsaro dukkan goyon bayan da ya wajaba don hana abuwar irin wadannan hare-hare nan gaba.
Daga nan ya mika sakon jaje ga iyalan wadanda wannan lamari ya shafa tare da fatan Allah ya gafarta musu,sannan ya ce wajibi ne su yi dukkan abin da ya dace don ganin an kare rayukan matasa kasancewarsu manyan gobe.
Wani dalibi da ya tsallake rijiya da baya, ya shaidawa Xinhua ta wayar tarho cewa, maharan sun rika harbi ne ta ko'ina,inda ya ce wadanda suka tsira sun fantsama cikin daji ne domin neman tsira da rayukansu.
A jawabinsa yayin da ziyarci asibitin garin Damaturu don jajantawa wadanda suka jikkata tare da duba gawawwakin wadanda suka mutu a harin,gwamna Ibrahim Geidam na jihar Yobe, ya yi alkawarin cewa, gwamnatin za ta dauki nauyin biyan kudin jinyar wadanda suka jikkata a harin na ranar Lahadi.
A cewarsa,dalibai 5 sun samu mummunan rauni, ciki har da guda 3 da suka samu karaya,kana guda ya samu raunin harbin bindiga, guda kuma ya samu rauni a kugunsa.
Wannan hari dai ya zo ne kwanaki kadan bayan da aka bude makarantu a jihar,kuma kwalejin yana daga cikin makarantun da gwamnatin ta rufe na tsawon makonni 10,bayan wani harin da ake zargin kungiyar Boko Haram ce ta kai a ranar 6 ga watan Yuli a garin Mamudo,inda aka halaka a kalla dalibai 29 da malami 1.
Jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya,tana daga cikin jihohi uku da shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana dokar ta baci a watan Mayu,inda aka tura dubban dakaru zuwa yankin don fatattakar 'yan kungiyar ta Boko Haram da ke hankoron ganin an shimfida shari'ar musulunci tare da yaki da ilimi Boko.
Tun da farko sai da gwamna Ibrahim Geidam na jihar ta Yobe, ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da shugabannin rundunonin tsaro, da su dauki matakan gaggawa don kawo karshen yawan hare-hare da kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba da ake yi a jihohin Borno da Yobe. Gwamna Geidam ya bayyana cewa,yawan rayukan da maharan ke hallaka a jihohin Yobe da Borno ya yi yawa.
Sai dai a jawabin da shugaba Jonathan na Najeriya ya yi ta talabijin a ranar Lahadi da maraice,yayin zantawar sa da manema labarai,ya ce hakika wadannan maharan basa kaunar hadin kai da ci gaban Najeriya.
A cewar shugaba Jonathan,manufar irin wadannan bata gari da marasa kishi da wadanda ke mara musu baya wajen kai wadannan hare-hare, shi ne mayar da hannun agogo baya ga ci gaban da wannan gwamnati ta samu a yakin da ta ke yi da ayyukan ta'addanci a kasar.
Ya yanzu dai kasashen duniya na ci gaba da aiko da sakon ta'aziya ga iyalan wadanda suka mutu ko suka jikkata tare da yin Allah wadai da wannan danyen aiki.
A nasa sakon,kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei, ya ce ko kadan kasar Sin ba ta amince da duk wani nau'i na ta'addanci ba,kuma a shirye take ta yi musayar fasahohin yaki da ta'addanci da yin hadin gwiwa da sauran kasashe, a kokarin da ake na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
Ita ma kungiyar tarayyar Turai,a sanarwar da Catherine Ashton manzon kungiyar a Najeriya,ta bayar,ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan wannan hari,inda ta bayyana kisan kiyashin a matsayin wanda bai dace ba.
Ashton ta kuma nanata kudurin kungiyar na baiwa kasar dukkan goyon bayan da ya dace, don ganin an yaki ayyukan ta'addanci kamar yadda dokokin kare hakkin dan adam suka gindaya. Tana mai cewa, maharan sun yi niyyar kaiwa yara da dalibai hari ne,kuma kamata ya yi a zakulo tare da hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki.
Shi ma ministan harjokin wajen kasar Canada, ya bayyana jajen kasarsa ga wadanda suka jikkata da iyalai da abokan wadanda suka rasa rayukansu a harin na garin Gujba.
Haka ma ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja, ya bayyana damuwarsa matuka da wannan hari a sakon da ya aike a shafinsa na twiter,inda ya ce suna tare da dukkan 'yan Najeriya a wannan lokaci na bakin ciki.(Ibrahim)