Ranar 17 ga wata a birnin Vienna na kasar Austriya, babban jami'in hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA) Yukiya Amano ya nuna cewa, ko da yake, ba a samu ci gaba mai kyau kan batun nukiliyar Iran ba, amma hukumar za ta ci gaba da yin shawarwari da kasar.
A gun taro karo na 56 na IAEA da aka kira a wannan rana, Yukiya Amano ya ce, game da batun ba da tabbaci ga wasu batutuwa kan kasar Iran, kasar Iran ba ta hada kai da hukumar yadda ya kamata ba, abin da ya sa IAEA ba za ta iya tabbatar da cewa, shirin nukiliya na Iran na zaman lafiya ne. Haka kuma, ya yi kira ga kasar Iran da ta hada kai da hukumar, ta yadda bangarorin biyu za su fara warware batun nan da nan.
Shugaban hukumar makamashin nukiliyar kasar Iran Fereydoun Abbasi Davani wanda ya halarci taron, ya yi jawabi, inda ya aza ayar tambaya ga zummar wasu kasashen yamma na neman warware batun nukiliyar kasar Iran. Kuma ya nuna cewa, wasu 'yan ta'adda da 'yan aware sun kutsa cikin IAEA sannan suna baya suna zuga wajen dagula al'amura a cikin hukumar, kuma sun yi habaici wai ya kamata hukumar IAEA ta dauki alhaki kan harin da aka kaiwa na'urorin nukiliyar kasar Iran.(Amina)