in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yabawa cigaban da hukumar IAEA ta samu kan tsaron makamashin nukiliya
2012-11-30 10:56:09 cri

Zaunanen wakilin kasar Sin a MDD Cheng Jingye ya bayyana a ranar Alhamis a birnin Vienna cewa, an samu babban cigaba wajen aiwatar da tsarin aiki na tsaron makamashin nukiliya na hukumar makamashi ta duniya IAEA.

A yayin wani zaman taro na manyan jami'an hukumar IAEA, mista Cheng Jingye ya bayyana cewa, an samu cigaba sosai tun lokacin da aka amince da wannan shiri na tsaron makamashi a yayin babban taron hukumar IAEA a shekarar 2011.

Mista Cheng ya jaddada cewa, IAEA tana da babban matsayi bisa bunkasa aikin tsaron makamashin nukiliya na kasa da kasa, kuma gwamnatin kasar Sin za ta cika alkawuranta tare da cigaba da tallafawa wannan shiri na IAEA kan tsaron nukiliya.

Gwamnatin kasar Sin na ba da babban muhimmanci ga tsaron nukiliya, kuma tana daukar wannan batu a matsayin aikin farko ga duk wasu tsare-tsare ko wasu ayyukan da suke da nasaba da nukiliya.

Hakazalika kuma taron zai tattaunawa kiyayewa, tsaro da sanya ido kan bangaren makamashin nukiliya, wannan kuma har da batun nukiliya na kasar Iran.

Kasar Sin kuma ta nuna fatan alheri ga shawarwari masu zuwa tsakanin kasar Iran da hukumar IAEA da za su gudana a wata mai zuwa kuma tana fatan bangarorin biyu za su cimma tudun dafawa, ta yadda za'a cimma yarjejeniya, in ji tawagar kasar Sin dake halartar wannan taron na kwamitin shawara na gwamnonin hukumar IAEA. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China