An kammala jefa kuri'un ne da karfe 10 na daren ranar Alhamis 18 ga wata. Kuma a yau Jumma'a 19 ga wata, aka bayar da sakamakon zaben, inda aka nuna cewa, kashi 55 cikin dari na masu jefa kuri'un sun ki amincewa da 'yancin yankin na Scotland a matsayin kasa mai cin gashin kanta.
Bisa kididdigar da aka yi, kashi 97 cikin dari na al'ummar yankin da suka cancanci jefa kuri'un ne suka yi rajista, alkalumma na nuni da cewa, wannan shi ne adadin mafi yawa a tarihin zaben da aka taba samu a yankin. (Zainab)