A ranar 18 ga wata da safe a birnin London, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci dandalin tattaunawar hada-hadar kudi a tsakanin Sin da Ingila tare da yin wani jawabi.
A cikin jawabinsa, Li Keqiang ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun da suka wuce, an kara yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Ingila a fannin hada-hadar kudi, wannan ya zama wani muhimmin abu a cikin dukkan hadin gwiwarsu. Birnin London ya riga ya kasance daya daga cikin manyan kasuwannin kudin Sin a kasashen waje ban da nahiyar Asiya. A wannan karo, an sanar da kafa cibiyar kudin Sin dake birnin London, kuma za a yi ciniki a tsakanin kudin Sin da Pam kai tsaye. Ta haka za a kyautata kasuwar hada-hadar kudi, da rage hadari a ciniki, da kuma sa kaimi ga kara zuba jari da yin ciniki a tsakanin kasashen biyu.
Ministan kudin kasar Ingila George Osborne ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, hadin gwiwar hada-hadar kudi muhimmin kashi ne na hadin gwiwar dake tsakanin Ingila da Sin, kuma ana samun ci gaba a shekarun nan. Kasar Ingila tana son kara yin hadin gwiwa da kasar Sin, kuma tana fatan kudin Sin zai kara taka muhimmiyar rawa a tsarin kudin duniya. (Zainab)