Yayin ganawar tasu a jiya Talata a fadar firaministan kasar Ingila, Mr. Li Keqiang ya bayyana cewa, a halin da ke kasancewa na dogara da juna, da aiwatar da tsarin bai daya a duniya, musamman a fannin tattalin arziki, dangantakar dake tsakanin Sin da Ingila ta moriyar juna da wadda ke shafar duniya baki daya na da muhimmanci kwarai.
Mr. Li ya kara da cewa bisa tushen girmama da juna, da samar da daidaito tsakani, kamata ya yi kasashen biyu su yi la'akari da abubuwan da suka jibance su, su kuma tabbatar da tushen siyasa, don baiwa kasashen biyu damar bunkasuwa, tare da kuma inganta dangantakarsu cikin sauri.
A nasa tsokaci Mr. Cameron ya amince da shawarar Li Keqiang game da inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. Yana mai cewa, kasarsa na dora muhimmanci sosai ga dangantakar dake tsakaninta da Sin, tare da fatan sassan biyu da su ci gaba da girmama da juna, da yin shawarwari, da kuma kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da hada-hadar kudi, da kimiyya da fasaha, da samar da wutar lantarki ta makamashin nukiliya, da kuma fannin sufurin jiragen kasa masu sauri da dai sauransu. (Zainab)