in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Minisatan wasannin Mozambique ya bukaci 'yan wasan kasar su kara kaimi
2014-08-15 09:33:28 cri

Ministan ma'aikatar wasanni da matasa a kasar Mozambique Fernando Sumbana, ya bukaci 'yan wasan kasarsa da suka samu zarafin lashe lambobin yabo a gasar Commonwealth, da su kara kwazo wajen samun karin nasarori a gasar Olympics da Brazil za ta karbi bakunci shekaru biyu masu zuwa.

Sumbana wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis din da ta gabata a birnnin Maputo, ya yin da yake maraba da 'yan wasan kasar da suka ciwo lambobin Azurfa da Tagulla, ya kara da cewa nan da shekaru biyu masu zuwa za a gudanar da gasar wasannin Olympic a Brazil, gasar da za ta zama karin dama ga matasan 'yan wasan kasar.

Ya ce yana cikin burin su, a kara yawan 'yan wasan da suke wakiltar kasar, kana 'yan wasan su kara yawan lambobin yabon da kasar ke lashewa.

Daga nan sai Sumbana ya ce duk da matsalolin da aka fuskanta, 'yan wasan kasar sun yi rawar gani, lamarin da a cewar sa ya dace da halayyar kishi da al'ummar kasar ke da shi na cimma dukkanin burin da suka sanya gaba. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China