A cikin jawabin fatan alheri, da shugaban kwamitin raya hakkin dan Adam na kasar Sin Luo Haocai ya karanto, ya bayyana cewa, hakkin dan Adam ya shafi tattalin arziki, da siyasa, da zaman al'umma, da al'adu da dai sauransu, kafa wani tsari mai kyau don raya hakkin dan Adam, da kawo yanayin inganta hakkin dan Adamu cikin dogon lokaci muhimmin aiki ne wajen kare hakkin dan Adam.
A nasa jawabi shi ma, direktan ofishin kula da yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin Cai Ming zhao ya ce, gwamnatin Sin ta mayar da girmama da kare hakkin dan Adam, a matsayin wata babbar ka'ida wajen mulkin kasar, kuma ta hada batun kare hakkin dan Adam da halin da kasar Sin ke ciki, don haka za a hada batun raya hakkin dan Adam, da batun raya tattalin arziki, da siyasa, da al'adu da zaman al'umma, da muhallin halittu tare, tana ta yin kokari wajen cimma burin samun bunkasuwa cikin dogon lokaci, ta hakan ne in ji shi za a raya batun kare hakkin dan Adam zuwa wani sabon matsayi.(Bako)