Yayin wannan taro mai taken "gina dauwamammen yanayin bunkasa harkokin kare hakkin dan Adam" an tattauna kan batuttuwan da dama, musamman batutuwa guda uku da suka hada da "doka da hakkin dan Adam", "gina zaman takewar al'umma da kare hakkin dan Adam", da kuma "tsaron yanki da kare hakkin dan Adam". A kwanaki biyu da suka gabata, wasu manyan jami'ai da masana kan hakkin dan Adam da suka halarci taron daga MDD, da kuma kasashe 33, da wakilan jakadun kasashen da abin ya shafa da ke nan kasar Sin, da wasu masanan hakkin dan Adam na kasar Sin kimanin 100, sun yi musayar ra'ayoyi kan batuttuwa daban daban a nan birnin Beijing. (Maryam)