in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF ta gabatar da kiran neman dala miliyan 200 domin murkushe cutar Ebola
2014-09-17 14:23:40 cri

Hukumar kula da kananan yara ta MDD UNICEF ta ce, tana bukatar fiye da dalar Amurka miliyan 200, domin ta samu sukunin daukar matakai na tunkarar barkewar cutar Ebola, wacce ta yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane 2,400 a Afrika ta yamma.

Wata majiya ta MDD ta yi nuni da cewar, kudaden da hukumar lafiya ta duniya ke bukata na daga cikin kudade da hukumomin jin kai na duniya ke muradi, a karkashin wani shirin neman taimako na watanni 6, wanda ke zimmar samar da taimakon kudade har dalar Amurka miliyan 987.8, domin taimakawa hukumomin MDD daukar matakai na murkushe cutar ta Ebola.

Darektan kula da ayyuka na gaggawa na hukumar ta UNICEF Afshan Khan ya ce, dole ne a dauki mataki a kan bala'in dake tattare da cutar Ebola, musamman saboda cutar ta yi sanadiyyar rufe makarantu, da dakusar da tsarin kula da lafiya, da kuma yin barazana ga daukacin al'umma. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China