in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta jinjina wa Sin game da gudumuwar da ta baiwa Afrika ta yamma wajen yaki da Ebola
2014-09-17 14:18:35 cri

Hukumar lafiya ta duniya a cikin wata sanarwa ta yi maraba da matakin sadaukarwa da gwamnatin kasar Sin ta dauka, a yayin da ta aike da wata tawagar kwararru wadanda ke gudanar da wata cibiyar binciken cututtuka na tafi da gidanka a kasar Saliyo dake Afrika ta yamma.

Matakin da kasar Sin ta dauka ya biyo bayan neman bukatar taimako daga gwamnatin Saliyo, da kuma wata kira da hukumar lafiya ta duniya ta yi, inda ta bukaci kasashe duniya da su ba da gudumuwa wajen daukar matakai na tunkarar cutar Ebola mai saurin kisan bil'adama.

Tawagar kwararrun daga kasar Sin za ta tallafa wa kasar ta Saliyo kokarin da take na tunkarar yaduwar cutar ta Ebola a asibitin hadin gwiwar abokantaka na Sin dake Saliyo, wanda aka gina a shekarar 2012 tare da taimakon kasar Sin.

Babbar darektan hukumar lafiya ta duniya Margaret Chan ta ce, bukata ta gaggawa da ake da ita a yanzu ita ce ta samar da karin ma'aikatan lafiya domin daukar mataki a kan cutar.

Chan ta kara da cewar, sabuwar tawagar daga kasar Sin za ta hade da wasu ma'aikatan lafiya kimanin 115, wadanda da dama sun dade da isa Saliyo domin ba da karfin gwiwar fuskantar kalubale na dakusar da yaduwar cutar Ebola. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China