Birnin Nairobi zai karbi bakuncin taron shiyya a ranakun Talata da Labara kan cutar Ebola, in ji ministan kiwon lafiyar kasar Kenya.
Mahalartan taron za su hada ministocin sufuri, kiwon lafiya, da fatauci na kasashe takwas da suka hada Burundi, Rwanda, Kenya, Tanzaniya, Uganda, DRC-Congo, Sudan ta Kudu da Habasha.
Makasudin wannan dandali shi ne na kawo wata amsar da ta dace cikin hadin gwiwa game da annobar cutar Ebola dake shafar wasu kasashen yammacin Afrika da dama, in ji ma'aikatar kiwon lafiyar Kenya a cikin wata sanarwa.
Haka kuma zaman taron zai hada wakilan hukumar kasa da kasa kan ci gaba (IGAD), kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) da kungiyar tarayyar Afrika (AU), ya biyo bayan taron da aka shirya a ranar 8 ga watan Satumba a Addis Abeba a karkashin jagorancin kungiyar AU.
A cikin sanarwata, ma'aikatar kiwon lafiyar Kenya ta jaddada muhimmaci ga gamayyar kasashen dake gabashin Afrika (CEA) dake kunshe da Kenya, Tanzaniya, Uganda, Burundi da Rwanda da su bullo da wata dubarar hadin gwiwa domin yaki da cutar Ebola, ganin yadda wannan cutar da zama wani babban bala'i da kuma yadda take yaduwa a wasu yankunan. (Maman Ada)