in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU na horar da ma'aikatan sa kai da za ta tura wajen yaki da cutar Ebola
2014-09-16 10:02:57 cri

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta bayyana a ranar Litini cewa, tana nan tana horar ma'aikatan sa kai kafin ta tura su wani aiki domin taimakawa yammacin Afrika yaki da cutar Ebola. Rukunin farko dake kunshe da ma'aikatan sa kai talatin da za'a tura Liberiya na samun horo a yanzu haka a cibiyar kungiyar AU dake birnin Addis Abeba na kasar Habasha, kuma za su tashi ranar Laraba.

AU na kuma shirin tura wani rukunin ma'aikatan lafiya da wasu kwararru domin yaki da annobar Ebola a yammacin Afrika, in ji wata sanarwa da kungiyar ta fitar.

Wadannan ma'aikatan sa kai sun hada da masana kan yaduwar cututtuka, masu bincike, kwararru a fannin lafiyar jama'a, da kuma ma'aikatan sadarwa. Kana sun fito daga kasashen Uganda, Rwanda, DRC-Congo, Najeriya da Habasha. Ayyukan nasu za su hada da karfafa karfin hanyoyi da dabarun cikin gida da na kasa da kasa, cike gibin kokarin da ake yi ta fuskar taimakon jin kai, da kuma daidaita tallafin kasashen da cutar ta fi shafa suka bayar, in ji AU. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China