Ministan lafiyar ya kuma bayyana cewa, ya zuwa ranar Asabar din da ta gabata, akwai mutane 66 da ko dai an tabbatar, ko kuma ana zaton sun dauke da cutar ta Ebola a kasar, kuma tuni 39 cikin wannan adadi suka rasu, ciki hadda jami'an jinya su 8.
Har wa yau ya ce cikin mutane 626 da a baya aka killace, an sallami mutane 342, yayin da ake ci gaba da sa ido tare da killacewa ragowar mutane 284.
Wannan ne dai karo na 7 da aka samu bullar cutar Ebola a kasar Congo Kinshasa, ko da yake hakan ba shi da nasaba da yaduwar cutar a kasashen Guinea, da Saliyo da sauran wasu kasashen yankin yammacin Afirka. (Zainab)