in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta Sin ya gana da mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar Mozambique
2014-05-27 14:46:32 cri
Shugaban majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar Sin Yu Zhengsheng ya gana da mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar Mozambique Shaomei La a yau Talata 27 ga wata a nan birnin Beijing.

Yayin ganawar ta su, Yu Zhengsheng ya bayyana cewa, Sin da Mozambique abokai ne a kowane hali, suna da dangantaka mai kyau kamar 'yan uwa. A cikin shekaru 39 da kafa huldar diplomasiyya a tsakaninsu, ana samun bunkasuwar dangantakar yadda ya kamata. Haka nan Sin ta dora muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakaninta da kasashen Afirka, za kuma ta kara hadin gwiwa a tsakaninta da Mozambique a dukkan fannoni bisa tsarin hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afirka. Kana za ta inganta dangantakar abokantaka dake tsakaninta da kasashen na Afirka.

Shi kuwa Mr Shaomei La cewa ya yi, majaliasar dokokin kasarsa za ta ci gaba da taimakawa wajen sada zumunci da kara hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Sin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China