A cewar rahotanni, an ce, an yi rikicin a wani gari dake lardin Inhambane a yankin kudancin kasar. Dakarun Renamo sun yi yunkurin sake kafa cibiyarsu dake lardin Inhambane wato kamar yadda ya faru a lokacin yakin basasan kasar, inda suka yi musayar wuta da sojojin gwamnatin, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan sanda 6, tare da jikkatar 'yan sanda 8, kuma dakarun Renamo guda 2 sun mutu cikin lamarin. Wasu kafofin yada labaru sun bayyana cewa, akwai fararen hula guda 2 da suka mutu a harin
Bayan da Mozambique ta samu 'yancin kai a shekarar 1975, dakarun Renamo suka rika daukar matakan soji kan sojojin gwamnatin, har zuwa shekarar 1992 da suka daddale yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin kasar. A ranar 21 ga watan Oktoba na bara, sojojin Mozambique suka mamaye sansanin Renamo da ke daji wato inda mafakar jagoran Renamo Alfonso Dhlakama, koda ya ke ya arce, daga bisani, jam'iyyar Renamo ta sanar da dakatar da wancan yarjejeniyar zaman lafiya.(Bako)