in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya jaddada muhimmancin sa kaimi ga samar da sabbin kayayyaki a duniya baki daya
2013-03-05 20:12:39 cri
A yammacin ranar Talata 5 ga wata, yayin da yake halartar taron rukunin Shanghai na NPC, babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS Xi Jinping ya jaddada cewa, kamata ya yi a nemi samun ci gaban ayyuka mai dorewa, da tsayawa tsayin daka kan bin hanyar gudanar da manufar yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, da kuma dora muhimmanci kan sa kaimi ga samar da sabbin kayayyaki.

Ban da haka, a yammacin wannan rana kuma, mataimakin firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci taron rukunin Shandong na NPC, inda ya furta cewa, cikin shekaru 5 da suka wuce, an sami babban ci gaba wajen zamanintar da zaman al'ummar kasar Sin, hakan ya dasa babban tushe wajen neman samun karin ci gaba. Idan ana son daidaita matsalolin da za a fuskanta a nan gaba, da ci gaba da sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki yadda ya kamata, dole ne a kara saurin canza hanyar bunkasa tattalin arziki, da samun daidaito tsakanin birane da kauyuka wajen samun bunkasuwa, ta yadda za a samu sabon tsarin ci gaba.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China