A ranar Laraba 6 ga wata, yayin da ake ci gaba da gudanar da babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a nan birnin Beijing, shugabannin kasar sun zanta da wakilan jama'a don tabbatar da manufofin kasar a fannoni daban daban.
Babban magatakardan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping, ya halarci taron tattaunawar da tawagar wakilan jama'ar lardin Liaoning suka kira, inda ya ce kamata ya yi a yi kokarin raya wasu tsoffin cibiyoyin masana'antun kasar da suka hada da yankin arewa maso gabashin kasar, sa'an nan a tabbatar da samun ingancin zaman rayuwar jama'a, sannan kuma su shaida moriyar da za a samar musu.
A nashi bangaren, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya halarci taron tawagar lardin Sichuan dake yammacin kasar Sin, inda ya ce wa'adin aikinsa na shekaru 10 zai kare, don haka yana yiwa jama'ar kasar godiya kan yadda suka ba shi damar bauta wa kasa, da karfafa masa gwiwa a lokacin da ya ke kula da ayyuka masu wuya. Ya ce yana fatan kasar za ta kara samun wata makoma mai kyau, kana jama'a za su kara samun jin dadin zaman rayuwa.
Ban da haka, shi kuma Li Keqing, mataimakin firaministan kasar Sin, ya halarci taron tawagar lardin Hunan, inda ya jaddada muhimmancin sauya hanyar da ake bi a kokarin raya kasa. A cewarsa, ya kamata a yi amfani da wasu sabbin ra'ayoyi, da kokarin hada burin raya tattalin arziki da na kiyaye muhalli waje daya, gami da nuna muhimmanci ga matsalolin da suka shafi jin dadin rayuwar jama'a, da kula da jama'ar dake cikin kangin talauci.(Bello Wang)