Bisa labarin da mataimakin magajin birnin Wuzhong Li Weining ya bayar, an ce, taron 'yan kasuwa na kabilar Hui da za a yi na wannan karo, ya kasance wani muhimmin kashi ne cikin taron baje-kolin kayayyaki da za a yi tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa, haka kuma, zai samar da wani dandanli ga birnin Wuzhong, don ya bayyana halin musamman da birnin ke ciki, kuma ya kara karfafa mu'amala da kasashen waje, da share fage don shirya taron hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa.
Bisa labarin da aka samu, an ce, a lokacin taron 'yan kasuwa na kabilar Hui, za a shirya taron shekara-shekara na kasuwanci na kabila ta Hui na shekarar 2013, da makon al'adu game da abinci na halal na duniya, da taron tattaunawa game da raya sana'o'insu, da taron ba da lambobin yabo ga masana'antun da suke yin kayayayyakin halal na duniya karo na 4 da taron kafa kungiyar yin magungunan kabilar Hui.
Tun daga shekarar 2008 kawo yanzu, ana cimma nasarar shirya taron 'yan kasuwa na kabila ta Hui har sau 5, baki sama da 300 da suka zo daga kasashen Larabawa cikinsu har da Saudiyya, da Masar, da wakilai sama da 6000 na Sin, sun halarci tarurrukan a baya, yanzu haka, wannan taro ya zama wani taron tattalin arziki da cinikayya da ya yi suna a gida da waje.(Bako)