in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara aikin hajji a Mecca
2013-10-13 17:31:15 cri
Ranar Lahadi 13 ga wata, musulmai kusan miliyan 2 da suka fito daga sassa daban daban na duniya sun taru a birnin Mecca na kasar Saudiya domin fara aikin hajji na tsawon kwanaki 5, kamar yadda su kan yi a ko wace shekara.

A kokarin tabbatar da gudanar da aikin hajjin yadda ya kamata a wannan shekara, gwamnatin Saudiya ta tura sojoji kusan dubu 100 domin yin rigakafin abkuwar manyan al'amuran ba-zata.

Sa'an nan kuma, manyan asibitoci guda 25 da asibitoci masu yawa da ke unguwoyi a birnin na Mecca a shirye suke wajen hana yaduwar cututtuka a tsakanin mutane.

A cikin dukkan musulman da suke yin aikin hajji a Mecca a bana, akwai musulmai kimanin dubu 11 da dari 8 da suka fito daga kasar Sin. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China