Kakakin sojan jihar Salah ad Din ya bayyana cewa, a wannan rana sojojin tsaron kasar Iraki sun yi nasarar shiga garin na Amirli mai nisan kilomita 90 daga gabashin birnin Tikriti bisa taimakon sojojin fararen hula na Shia da dakarun yankin Kurdawa fiye da dubu daya, Kana mayakan saman kasar Iraki da na kasar Amurka na taimaka musu ta sama.
Firaministan kasar Australia Tony Abbott ya bayar da wata sanarwa a ranar 31 ga watan Agusta cewa, bisa bukatar kasar Amurka, kasar Australia ta tsaida kudurin kai makamai ga arewacin kasar Iraki ta jiragen sama.
Ita ma gwamnatin kasar Jamus ta tsai da kudurin a ranar 31 ga watan Agusta don samar da makamai masu linzami na yaki da tankokin yaki da kuma bindigogi da dama ga Kurdawa dake arewacin kasar Iraki don yaki da kungiyar IS. (Zainab)